Jerin kasashen Duniya da su ka fi karfin fada a ji a yau
Jaridar Independent ta kawo jerin Kasashen da su ka fi kowane karfi a Duniya. Wannan ya sa mu ka tsakuro kadan daga cikin kasashe irin su Amurka da Sin da yanzu duk Duniya babu kamar su.
1. Kasar Amurka
A duk Duniya babu kasar da ke da iko da karfi irin Amurka. Wasu na ganin Amurka ta rasa martabar ta bayan hawan Shugaba Donald Trump kan mulki.
2. Kasar Rasha
Bayan Amurka, babu kasar da ke da karfi a Duniya irin Rasha. Kasar na da arziki da dama kuma tana da matukar karfin Soji wanda tayi fice ta nan a Duniya.
KU KARANTA: Wani Dan kasar Amurka zai leka Duniyar sama-jannati
3. Kasar Sin
Nan da 2050 ana sa rai babu kasar da sa ta sha gaban China ta fuskar tattalin arziki. Kasar Sin na da mutane da ke nema su kai Biliyan daya da rabi.
4. Kasar Birtaniya
Kasar UK ce gaba a Duniya bayan Amurka, da Rasha da kuma Sin. Ingila tana da karfin tattali da kuma tarihi. Sai dai yanzu kasar na cikin wani hali na siyasa.
5. Kasar Jamus
Jamus ce kan gaba a jerin kasashen Turai a Yankin ta. Kasar na da dinbin mutane kuma ta na kara karfi tun bayan dunkulewar kasar a shekarar 1990.
Bayan wadannan kasashe akwai irin su Farasa, Jafan, Israila, Koriya da irin su Saudi Arabia da su na cikin manya a Duniya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng