Son kai ya kai Obasanjo yi wa Buhari gangamin taron dangi, inji Edwin Clark

Son kai ya kai Obasanjo yi wa Buhari gangamin taron dangi, inji Edwin Clark

- Har yanzu dai yan Najeriya na cigaba da tofa albarkacin bakin su kan gangamin taron dangin da Obasanjo ke shirya wa Buhari

- Shugaban Kabilar Ijaw, Cif Edwin Clark ya cacaki Obasanjo inda ya ce Obasanjo ne sanadin suk matsalolin mulkin da muke fama da shi a kasar nan

- Haka zalika, Kungiyar matasan Arewa (ACF) ta shawarci Obasanjo ya kyale yan Najeriya sun zabi wanda suke so ya mulke su

Har yanzu, al'umma na ta tofa albarkacin bakin su kan gangamin taron dangi da Obasanjo ya kafa domin tabbatar da cewa Shugaba Muhammadu Buhari bai zarce a kan karagar mulki ba.

Hakan yasa shugaban kabilar Ijaw kuma dan gwagwarmayar yankin Neja-Delta, Cif Edwin Clark ya gargadi yan Najeriya da suyi takatsantsan da shawarwarin Obasanjo. A cewar sa, Obasanjo ne ummulaba'isin matsalolin shugabancin da muke fama da su a Najeriya.

Son kai ya kai Obasanjo yi wa Buhari gangamin taron dangi - Matasan Arewa
Son kai ya kai Obasanjo yi wa Buhari gangamin taron dangi - Matasan Arewa

A hirar da yayi da jaridar The Nation ta wayar tarho, Clark ya ce "Za mu yi amfani da shawarwarin da Obasanjo ya bayar amma dai shi bamu yarda dashi ba domin mun tabbatar manufar sa ba ta kirki bane"

KU KARANTA: Gwamnatin Najeriya tana neman sasauci ga 'yan Najeriya da aka yanke wa hukuncin kisa a Saudiyya

Haka zalika, Kungiyar matasan Arewa ta bukaci Obasanjo ya ja bakin sa yayi shiru ya kyalle yan Najeriya su zabi wanda suke so ya mulke su.

Kungiyar matasan Arewan ta kara da cewa Obasanjo ya mulki Najeriya ne shekaru takwas, kuma ya yi yunkurin kara wa'adin mulkin nasa sai dai hakan bai yiwu ba, kuma tun daga wannan lokaci Obasanjo bai dena tsoma bakinsa cikin harkokin mulkin Najeriya akasin yadda sauran tsaffin shugabanin kasa keyi.

Shima tsohon Gwamnan jihar Edo, Kwamared Adams Oshiomole ya tofa albarkacin bakin sa kan lamarin inda ya ce Obasanjo baya daya daga cikin masu bawa Buhari shawara saboda haka ya ja bakin sa ya yi shiru. Oshiomole ya kara da cewa Obasanjon bashi da nufi mai kyau a zuciyar sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164