Wani yaro da bai isa tuki ba ya halaka wata daliba da wadan su mutane biyu a Gusau

Wani yaro da bai isa tuki ba ya halaka wata daliba da wadan su mutane biyu a Gusau

- Wani yaro da bai isa tuki ba ya halaka wata daliba da wadan su mutane 2 kuma

- Wannan lamari ya faru ne a ranar Litini yayin da yaron ta babano mota kirar Marsandi

- Hukumar 'Yansanda su na gudanar da bincike game da lamarin a halin yanzun

Kamfanin Dillancin Labarai (NAN), ta ruwaito cewar wani yaro da bai isa tuki ba ya halaka mutane 3 a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara. A na zargin yaron da yin tukin ganganci.

Cikin mutanen da ya halaka har da wata dalibar Makarantar Horas da Malaman Asibiti da Unguwan Zoma na Jihar. Wannan lamari ya faru ne a ranar Litini. Wata majiya da ta nemi a sakaya sunan ta, ta bayyana cewar yaron ya sharo gudu ne cikin mota kirar Marsandi.

Direba da bai isa tuki ba ya halaka rayuka 3 a Gusau, ciki har da dalibar shekaran karshe
Direba da bai isa tuki ba ya halaka rayuka 3 a Gusau, ciki har da dalibar shekaran karshe

KU KARANTA: Kotu ta yankewa 'yan kasuwan man fetur 2 shekaru 8 a gidan yari bisa cuwacuwan mai na N789.6m

Hukumar 'Yan Sandan Jihar ta tabbatar da faruwar lamarin ta baki mai magana da yawun ta, DSP Mohammed Sani. Hukumar ta ce ba a kai ga kama yaron ba amma an samu bayanai game da shi kuma a na gudanar da bincike.

Ita ma Hukumar Kiyaye Dokokin Kan Titi (FRSC), ta shaida faruwar lamarin. Ta kuma ce a halin yanzun lamarin ya na hannun Hukumar 'Yansanda. Mai magana da yawun Hukumar, Malam Nasir Ahmad, shi ne ya shaida hakan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164