A matsayi na a Majalisa, Sakarcin banza ne Gwamnati ta maka ni a Kotu – Saraki

A matsayi na a Majalisa, Sakarcin banza ne Gwamnati ta maka ni a Kotu – Saraki

- Shugaban Majalisa Saraki yace bai dace a rika katsalandan a Gwamnati ba

- Bukola Saraki yace doka ta ba ‘Yan Majalisa damar gudanar da sha’anin su

- A baya dai an ta shiga Kotu da Sanatan wanda yace hakan sam bai dace ba

Mun samu labari cewa Bukola Saraki ya caccaki Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta bakin Sakataren sa Sanni Onogu a kwalejin Sojojin kasar inda yace sam bai kamata Gwamnati ta kai shi Kotu ba bayan ya zama Shugaban Majalisar Dattawa.

A matsayi na a Majalisa, Sakarcin banza ne Gwamnati ta maka ni a Kotu – Saraki
Saraki yace Majalisa na da hurumin cin karen ta babu babbaka

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki a wata takarda da ya gabatar yace babban abin da ke rike tsarin Damukaradiyyar kasar nan shi ne ba kowane bangare na Gwamnati damar aikin sa. Saraki yace duk tare ake tafiya da masu zartawa da masu sharia.

KU KARANTA: Kwankwaso ya bayyana abin da zai rusa Jam'iyyar APC

Saraki ya soki kalaman Sakataren Gwamnatin Tarayya game da kalaman sa bayan da Majalisar tace ba za ta tantance wadanda Shugaba Buhari ya nada ba saboda wata takkadama. Saraki yace doka ta ba su dama su dauki wannan mataki da su ka dauka.

Bukola Saraki yace sakarci ne Gwamnati ta maka su a Kotu bayan da ya ci zabe don kuwa Sanatoci da sauran ‘Yan Majalisu su na damar cin karenn su ba babbaka kamar yadda tsarin mulki ya tanada. Shugaban Majalisar yace dole Jama’a su fahimci wannan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng