Gwamnatin jihar Sokoto za ta gina katafaren kamfanin Sarrafa suga
A yunkurin ta na samar da ayyuka da inganta rayyuwan al'ummar jihar, Gwamnatin jihar Sakkwato karkashin jagorancin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal za ta gina wata katafare kamafanin sarrafa Suga a jihar ta Sakkwato.
Gwamnatin jihar za ta yi hadin gwiwa ne da wata kamfanin mai zaman kanta domin ginin kamfanin.
Wanda suka hallarci taron rattafa hannu kan yarjejeniyar da Gwamna sun hada da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, Karamar Ministan kasuwanci da saka hannun jari, Aisha Abubakar da kuma jami'an Hukumar Suga na Kasa.
KU KARANTA: Dalilai hudu da ke sa 'yan Najeriya bijirewa kayayakin mu na gida
Ana sa ran kamfanin zai samar da aiki ga dimbin matasa da kuma bunkusa harkokin kasuwanci a jihar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng