Za a zauna game da batun Hijabi a Makaruntun Layoyin Najeriya

Za a zauna game da batun Hijabi a Makaruntun Layoyin Najeriya

- Za a zauna a Majalisa game da batun Misis Firdausi Amasa a makon nan

- Kwanakin baya an haramtawa Amasa zama Lauya saboda ta sanya Hijabi

- ‘Yan Majalisa sun kira zama domin shiga cikin rikicin Musulamar ‘Dalibar

Mun samu labari daga Jaridun kasar nan cewa kwamitin shari’a na Majalisar Wakilai na Tarayya sun kira zama na musamman a kan maganar wata ‘Daliba da aka haramtawa sa hijabi a kwanakin baya a Makarantar Lauyoyi na Najeriya.

Za a zauna game da batun Hijabi a Makaruntun Layoyin Najeriya
Majalisa za ta shiga cikin rikicin Hijabi a Makarantar Lauyoyi

Za a zauna ne a Majalisar game da batun amfani da Hijabi a Makaruntun Layoyin Najeriya da sauran wurare a Ranar 26 ga wannan wata. Ana kuma kira ga jama’an da ke da korafi ko ta-cewa su aikawa Majalisar ra'ayin su domin tattauna batun.

KU KARANTA: Inyamuran Najeriya za su goyi bayan Shugaba Buhari

A baya an ta ce-ce-ku-ce kan wata ‘Daliba mai suna Firdausi Amasa da tubure sai ta sa Hijabin ta a Makarantar Lauyoyin kasar. Yanzu haka Majalisar Tarayyar ta gayyaci Ministan shari’a da kuma Kungiyar Lauyoyin kasar da Misis Amasa.

Bayan nan kuma kwamitin Majalisar na gayyatar sauran masu ruwa da tsaki a kan harkar irin su Makarantar sanin aiki na karatun Lauya na kasar da ta haramtawa Firdausi shiga cikin sahun Lauyoyi saboda ta rantse cewa ba za ta cire Hijabi ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng