Wani babban Dogarin Gwannan Jihar Borno ya rasu

Wani babban Dogarin Gwannan Jihar Borno ya rasu

- Gwamna Kashim ya rasa wani babban Dogarin sa jiya

- Babban 'Dan Sandan ya cika ne bayan wata rashin lafiya

- Za a bayyana lokacin da za a birne Mariayin a yau dinnan

Labari maras dadi ya kai gare mu cewa Gwamnan Borno Alhaji Kashim Shettima yayi babban rashi a farkon makon nan na rasa wani babban Dogarin sa wanda ke masa hidimar aiki.

Wani babban Dogarin Gwannan Jihar Borno ya rasu
Mai girma Gwannan Jihar Borno Kashim Shettima

Jaridar Yerwa Express ta bada wannan rahoto a Yammacin jiya Litinin dinnan. Wani Dogarin Gwannan Jihar Borno Kashim ne ya rasu bayan yayi fama da 'yar rashin lafiya na wani lokaci inji Majiyar ta mu daga Jihar.

KU KARANTA: An aika sabon kwamishinan 'Yan Sanda zuwa Benuwe

Babban Jami’in Mohammed Azare wanda yana cikin Dagoran 'Yan Sandan Mai Girma Gwamnan Jihar yace ga garin ku nan bayan yayi fama da rashin lafiya inji Darektan yada labari na Gwamnatin Jihar Alhaji Ali Chiroma.

Dogarin ya rasu ne a jiya Litinin kuma ana sa ran ba da dadewa ba za a birne sa Inji Jami'in yada labarai na gidan Gwamnatin Jihar watau Ali Chiroma.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel