Yadda ta kaya a ziyarar da Kwankwaso ya kai ma Buhari a fadar shugaban kasa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a daren Alhamis, 18 ga watan Janairu, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.
Tsohon gwamnan na jihar Kano ya kai ziyarar ne bisa gayyata da shugaban kasa ya aika masa, tare da sauran shuwagabannin jam’iyyar APC, inda ya shirya musu liyafar cin abinci.
KU KARANTA: Buhari ya lashi takobin ladabtar da duk masu shirin tayar da zauni tsaye a 2019
Cikin tawagar da suka halarci taron akwai shugaban jam’iyyar APC, John Oyegun, Sakataren jam’iyyar APC,Mai Mala Buni, tsohuwar yar gwagwarmaya Naja’atu Muhammad, tsohon gwamnan jihar Abia,Orji Uzor Kalu.
Sauran sun hada da tsohon gwamnan jihar Ekiti, Segun Oni, tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani, tsohon gwamnan jihar Nassarawa, Abdullahi Adamu, Sanata Aliyu Wammako, Abba Kyari da kuma sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha.
Rahotanni sun yi bayanin cewa shugaban Buhari tare da jiga jigan na jam’iyyar APC sun tattauna ne kan batutuwan da suka shafi al’amuran siyasa, musamman zaben 2019, da kuma hanyoyin cigaban jam’iyyar tasu, dama cigaban Najeriya gaba daya.
Ga sauran hotunan:
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng