'Yan bindiga sun harbe wani jami'in tsaro a jihar Katsina
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, wani karamin jami'in dan sanda, Ibrahim Surajo, ya riga mu gidan gaskiya a yayin da 'yan bindiga dadi suka bude masa wuta a jihar Katsina tare da yin awon gaba da bindigarsa ta aiki.
Wannan lamari ya faru ne da misalin ƙarfe 8:30 na daren ranar da ta gabata, inda Surajo ya yi kacibus da ajali yayin da yake bakin aikinsa a cikin birnin na Katsina.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Gambo Isa ya tabbatar da faruwar wannan lamari da cewar 'yan bindigar sun zo ne wata mota kirar Golf Volkswagen baƙa ƙirin.
Surajo dai ya ɗan gusa kaɗan zuwa wani shago dake daura da inda suke aiki domin tsotsawa wayarsa ta salula caji, sai kuwa 'yan bindiga suke buɗe masa wuta inda ko shurawa bai kuma ba.
DSP Gambo ya bayyana cewa, hukumar ta samu wani muhimmin rahoto wanda zai taimaka musu wajen ci gaba da gudanar da bincike tare da damko waɗanda suka yi wannan aika-aika.
KARANTA KUMA: Badaƙalar N92m: Hukumar EFCC ta cafke ɗan tsohon gwamnan jihar Nasarawa
A baya dai makamancin wannan hari ya afku, inda aka harbe wani jami'in dan sanda, Musa Ibrahim har lahira tare da yin awon gaba da bindigarsa ta aiki, a yayin da tartsatsin harsashi ya raunata wani karamin ma'aikaci, Shitu Maikudi.
Legit.ng ta fahimci cewa, wannan hari ya afku ne a gidan tsohon sufeto janar na 'yan sanda, Ibrahim Coomassie, a watan Oktobar shekarar da ta gabata.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng