Yadda kwararowan ruwa daga wani Dam ke barazana ga rayuwar mutane a Kaduna

Yadda kwararowan ruwa daga wani Dam ke barazana ga rayuwar mutane a Kaduna

- Mazauna wasu kauyukan jihar Kaduna guda sun koka bisa tsagewar gabar wani Dam

- Sun nemi taimakon gaggawa daga gwamnati da kuma kungiyoyi masu aikin jin kai

- Mai taimakawa gwamna Nasir El-Rufa'i ya dauki alkawarin sanar da gwamnan halin da ake ciki

Mazauna wasu kauyukan jihar Kaduna shida sun koka bisa barazanar da zabtarewan gabar wani babban Dam ke yi ga rayuwar su, tare da neman agajin gaggawa daga gwamnati da kuma kungiyoyi masu zaman kansu.

Kauyukan dake fuskantar wannan barazana sun hada da; Gobirawa, Ruhogi, Barkonu, Cikaji, Likoro da Unguwar Yamman Likoro, da Girkawa, dukkaninsu a karamar hukumar Igabi dake jihar Kaduna.

Yadda kwararowan ruwa daga wani Dam ke barazana ga rayuwar mutane a Kaduna
Gwamnan Jihar Kaduna
Asali: UGC

Wani mazaunin kusa da Dam din kuma shugaban kungiyar masunta, Malam Usman Jikan Mudi, ya ce Dam din ya samu matsala sakamakon ruwan damina mai dumbin yawa da ya kwaranya cikinsa.

Jikan Mudi ya ce "Dubban jama'a ne da iyalansu ke cikin fargaba da tashin hankali sakamakon zabtarewan gabar Dam dim, hakan ne ya saka muke ankarar da hukuma halin da muke ciki domin daukan matakan kiyaye afkuwar kwararowan Dam din ya zuwa cikin Kauyukan mu."

DUBA WANNAN: Gwamnatin jihar Kaduna za ta kashe N337.19m domin horar da malaman makarantu

Jikan Mudi ya ce a baya sun rubuta takardun koke zuwa ga gwamnati amma ba'a yi komai a kai ba. Hakan ya saka yanzu suke neman taimako daga kungiyoyi masu zaman kansu.

Mai Unguwar garin Gobirawa, Umaru Gobirawa, ya ce lokacin da gabar Dam din ya fara tsagewa, a watan Oktoba na shekarar 2017, jama'ar garin basa iya bacci da idanuwansu biyu a rufe.

Da yake magana a madadin gwamnati, mai taimakawa gwamnan jihar Kaduna a bangaren yada labarai, Saidu Adamu, ya bayar da tabbacin sanar da gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufa'i, halin da al'ummar kauyukan ke ciki domin daukar matakin gaggawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng