Ba mu da filayen kiwon shanu, in ji Gwamnatin Jihar Taraba
- Gwamnatin Jihar Taraba ne ta bayyana hakan ta bakin Alkalin Alkalan Jihar, Yusufu Akirikwen
- Jihar ta fitar da doka na samar da filayen kiwo ga makiyaya, dokar za ta fara aiki ne 24 ga watan Janairu
- Ta ce makiyaya za su sayi filaye ne domin kiwo kamar yadda manoma ke sayan filayen noma
Gwamnatin Jihar Taraba ta bayyana cewar ba ta da filayen da za ta kebe domin makiyaya su yi kiwon shanayen su kamar yadda Gwamnatin Tarayya ta bukaci Jihar ta yi.
Jihar ta yi wannan bayani ne a ranar Laraba ta bakin Alkalin Alkalai kuma Kwamishinan Shari'a na Jihar, Yusufu Akirikwen, yayin ganawar sa da Jaridar Punch a Jalingo.
DUBA WANNAN: Kannywood ta horas da matasa 450 harkar shirya fim
Akirikwen ya bayyana cewar Jihar ta fitar da doka na samar da filayen kiwo ga makiyaya wanda zai fara aiki a ranar 24 ga watan Janairu. Sakamakon haka ne ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta tallafa don ganin wannan doka ya zauna.
A cewar sa, wannan shi ne hanya mafi inganci da duniya ta rike na kiwon shanaye. Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta samar da tsaro don ganin wannan doka ta zauna. Don kuwa ya ce ta na da babbar rawa da za ta taka game da wanzuwar dokar.
A bayanin da ya yi, makiyaya za su sayi filayen kiwo ne da Gwamnati ta tanadar kamar yadda manoma ke sayen filaye don noma.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng