Kungiyoyin Musulmai sun gwabza a kan lokacin Sallar juma’a, mutum 1 ya mutu

Kungiyoyin Musulmai sun gwabza a kan lokacin Sallar juma’a, mutum 1 ya mutu

Akalla mutum guda daya ne ya rasa ransa a wani rikici daya barke tsakanin kungiyoyin addinin Musulunci, da suka kunshi, Izala da na Darika, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya tabbatar.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a karamar hukumar Munya na jihar Neja, inda kungiyoyin suke rike da bambamcin ra’ayi dangane da lokacin gudanar da Sallar Juma’a.

KU KARANTA: Yan majalisu sun wasa wukarsu don bincikar dala miliyan 44 da suka ‘ɓace’ a hukumar liken asiri

Hakazalika majiyar ta cigaba da da fadin Karin rikicin shine yanke shawara da kungiyar Izalan jihar ta yin a cewa zata bude masallacin ta na juma’a daban da wanda ya darikan ke amfani da shi a garin, wanda hakan yayi sanadiyayr fito na fito da muggan makam tsakanin mabiyan kungiyoyin.

Kungiyoyin Musulmai sun gwabza a kan lokacin Sallar juma’a, mutum 1 ya mutu
Rikici

Kaakakin rundunar Yansandsan jihar ASP Abubakar Dan-Ina ya tabbatar da faruwa lamarin, inda yace tuni an aika da jami’an rundunar Yansanda don tabbatar da zaman lafiya, sai dai ko da isarsu, sai wani bangare na jama’an suka fada musu da adduna da sauran makamai, inda suka jikkata Dansanda guda.

Daga karshe Kaakakin ya tabbatar da kama mutane 28 dake da hannu cikin rikicin tare da kai ma jami’an Yansandan hari, yayin da rudunar ta kaddamar da bincike don tantance gaskiyar lamarin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng