Sufetan ‘Yan Sanda Ibrahim Idris zai shiga Arewo maso gabas
Sufeta Janar na ‘Yan Sandan Najeriya Ibrahim Idris zai leka Yankin Arewa-maso-gabashin Kasar nan inda aka yi fama da rikicin Boko Haram kamar yadda mu ka samu labari.
Rudunar ‘Yan Sandan Najeriya za ta leka Yankin Boko Haram inda Shugaban ‘Yan Sandan Kasar Ibrahim Idris da kan sa zai jagoranci tawagar Gwamnatin Tarayya domin ganewa idanun sa.
Sufeta Janar na ‘Yan Sandan kasar Ibrahim Idris zai leka Yankin Arewa maso gabashin Kasar inda rikicin Boko Haram yayi kamari a kwanakin baya. IG na ‘Yan Sandan kasar ya bayyana wannan ne ga wani gidan talabijin na kasar.
KU KARANTA: Karin matsayi: Kemi Adeosun ta samu mukami a UN
Yanzu haka Shugaban ‘Yan Sandan Kasar yana Yankin Arewa maso tsakiyar kasar kamar yadda aka ba sa umarni. Rikicin Yankin ya sa Shugaban ‘Yan Sandan ya dawo aiki taka-nas zuwa Garuruwan Logo da Guma da ake ta’asa.
Idan ba ku manta ba kwanan nan Shugaban Kasa Buhari ya umarci Shugaban ‘Yan Sandan kasar ya koma Yankin Benuwe da rikicin Makiyaya da ‘Yan Gari.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng