Gobara ta cinye matar aure a Bauchi har saida dan cikinta ya fito
- Gobara yayi sanadiyar mutuwar wata mata aure ma juna biyu a jihar Bauchi
- Wutan gobarar da ya kona mata mai juna biyu a jihar Bauchi yasa jaririn dake cikin ya fito waje
Wutan gobara da ya babbaka wata mata mai juna biyu, ya sa jaririn dake cikin ya fito waje a unguwar Kandihar dake jihar Bauchi.
Wani bawa Allah mai suna, Abubakar Ubayo, ya bayyana aukuwan wannan mumunar lamari a shafin sa na Facebook.
Abubakar Ubayo, ya rubuta a shafin sa na Faceebook kamar haka, “Inalillahi Wa’innailaihi Raji’un wannan matar wani abokin mu ne mai suna Auwal wacce take ‘dauke da juna biyu, kuma wannan watan shine watan haihuwar ta.
"Allah a cikin ikon shi, sai gashi sun hadu da jarabawar gobara a gidan su ya kona matar sa, har sai da jaririn dake cikin ta ya fito waje.
KU KARANTA : Yanzu Yanzu: Kotun daukaka kara ta dakatar da dan majlisa, ta yi umurnin sake sabon zabe
Har yanzu Legit.ng Hausa bata samu cikakken labari game da musabbabin tashin gobarar ba.
Ubangiji Allah muke roko ya karbi shahadar ta, ya kuma gafarta mata kurakuran ta.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng