Yanzu Yanzu: Kotun daukaka kara ta dakatar da dan majlisa, ta yi umurnin sake sabon zabe

Yanzu Yanzu: Kotun daukaka kara ta dakatar da dan majlisa, ta yi umurnin sake sabon zabe

- Wata kotun daukaka kara ta soke zaben Mansir Aliyu Mashi (APC) dake wakiltan mazabar Mashi/Dutsi na jihar Katsina

- Ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta da ta gudanar da sabon zabe a mazabu 15

- Justis Abba Aji a shari’’arsa ya ce anyi magudin zaben a wadannan mazabu da ake Magana akai

Wata kotun daukaka kara ta dakatar da Mansir Aliyu Mashi daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) dake wakiltan mazabar Mashi/Dutsi na jihar Katsina.

Legit.ng ta tattaro cewa an umurci hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ta gudanar da sabon zabe a mazabu 15 inda akayi magudin zaben.

Yanzu Yanzu: Kotun daukaka kara ta dakatar da dan majlisa, ta yi umurnin sake sabon zabe
Yanzu Yanzu: Kotun daukaka kara ta dakatar da dan majlisa, ta yi umurnin sake sabon zabe

Kotun zabe dake Katsina ta soke zaben Mashi bayan an kawo cewa anyi magudin zaben, da kuma kwace akwatin zabe da kuma hana gudanar da zabe a wasu mazabu sannan kuma ta yi umurnin sake zabe a wadannan mazabu.

KU KARANTA KUMA: Yadda mu ka kama Desmond Okutubo, babban dan kungiyar Don Wanny – Yan sanda

Jagoran kotun daukaka karan, Kaduna, Justis Umani Abba Aji a hukuncin da ya yanke a ranar Juma’a, 12 ga watan Janairu ya ce, sashin hukunci sunyi adalci a hukuncinsu, wanda ya soke zaben wanda ya zo na farko, Mansur Aliyu Mashi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel