Rashin Tausayi: An gano kokon kan wani jami'in dan sanda a gidan tsafi
- Rundunar yan sanda sun kama wani Hakimin kauye da wasu samari bisa laifin kashe jami'in dan sanda
- An kashe jami'in dan sandan, Michael James, ranar 25 ga watan Disambar 2017 yayin da yaje ziyarar surukin sa a garin Ojor
- Binciken rundunar yan sandan ne yasa suka gano kan dan sandan a gidan tsafi na garin kuma suka cafke wasu matasa dauke da bindigogi
Rundunar yan sandan reshen jihar Ribas ta cafke wani mutum mai shekaru 54, Valentine Ebani dauke da kokon kan wani jami'in dan sanda mai mukamin sifeta, Michael James wanda aka kashe kwanakin baya a garin Uyanga da ke karamar hukumar Akamkpa na jihar ta Ribas.
Bincike ya nuna cewa Ebani ne Hakimin kauyen Uyanga, har ila yau, shine mai kula da gidan tsafin garin. An kama shi tare da wasu mutane bakwai kuma ana tuhumar su da kisar jami'in dan sandan inda daga bisani su ka file kan sa suka kai gidan tsafin.
DUBA WANNAN: Rikicin Benuwe: Idan gwamnati ba za ta iya kare mu, za mu kafa namu sojojin - Unongo
An dai kashe James ne a ranar 25 ga watan Disambar 2017 yayin da rigima ya barke tsakanin garin Uyanga da makwabtan su na Ojor a karamar hukumar ta Akamkpa. A nan ne wasu matasa suka kai masa hari kuma suka kashe shi.
Kwamishinan yan sanda, Mista Hafiz Inuwa yace rigimar ta ritsa da marigayi James ne lokacin da ya kai iyalan sa kauyen Ojor wajen surukan sa ASP Dominic Umoh.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng