Zamfara: Gwamna Abdulazeez Yari yayi wa kwamishinoninsa garanbawul
- Gwamna jihar Zamfara yayi wa kwamishinonin sa garanbawul dan tabbatar da cigaba a jihar sa
- AbdulazeezYari ya canza wa wasu kwamishinoni sa ma'aikatar yayin da ya bar wasu akan mukamin su
Gwamnan jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari Abubakar, yayi wa gwamnatin sa garanbawul dan tabbatar da cigaba a jihar sa.
A jawabin da sekataren gwamnatin jihar Zamfara, Abdullahi Muhammad Shinkafi ya fitar, ya ce wasu kwamishinoni za su cigaba da rike mukamin su yayin da wasu za su koma sabbin ma’aikata a jihar.
Jawabin ya nuna, tsohon kwamishinan ma’aikatan kula da harkan ruwa, Alhaji Sanda Muhammad Danjari, ya zama sabon kwamishinan ma’aikatar watsa labaru da al’adu, sai kuma Umar Jibo Bukkuyum, ya zama kwamishinar ma’aikatar kula da harkan ruwa.
KU KARANTA : Akwai wadanda ake zargi da zama yan kungiyar Boko Haram guda 20,000 a cikin gidajen kaso a fadin kasar – Mansur Dan Ali
Tsohon Kwamishinan ma’aikatan raya karkara, Alhaji Lawal M. Liman ne sabon kwamishinan ma’aikatan kiwon lafiya, sai kuma tsohon Kwamishinan ma’aikatan kiwon lafiya, Alhaji Sule Adamu Gummi, ya koma ma’aikata filaye a matsayin sabon Kwamishinan yayin da Alhaji Idris Muhammad Keta ya zama sabon Kwamishinan mai’aikatan raya karkara da ci gaban al'umma daga ma'aikatar muhalli da kewaye.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng