Gwamna Masari ya barnatar da kudin jihar Katsina N400b - PDP
- Jam'iyyar PDP ta zargi gwamna Masari da barnatar da kudaden jihar Katsina
- Ta zarge shi da gaza tabuka wani abun kirki cikin fiye da shekaru biyu
- Gwamnatin jihar ta yi watsi da wannan zargin
Jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Katsina ta zargi gwamnan jihar, Aminu Bello Masari, da laifin barnatar da kudaden jihar da adadinsu ya kai biliyan N400 a cikin watanni 31.
Shugaban jam'iyyar PDP a jihar Katsina, Salisu Maigari, ne ya sanar da hakan a jiya Talata yayin tattaunawa da manema labarai.
Maigari ya ce jihar ta karbi kudaden ne daga gwamnatin tarayya amma maimakon yin abinda ya dace sai kawai jami'an gwamnati jihar suka barnatar da su ta hanyoyin da basu da ce ba tare da barin jihar cikin talauci da dumbin bashi.
DUBA WANNAN: Shirin S-Power na gwamnatin jihar Katsina zai samar da aiki ga masu kwalin NCE 5,000 - Gwamna Masari
A cewar Maigari, gwamnatin jihar ta karbi fiye da biliyan N243 daga asusun gwamnatin tarayya, sannan ta kara karbar biliyan N30 na Faris Kulob ga kuma bashi da ta karbo daga bankuna na biliyan N70, bayan tarin kudin da jam'iyyar PDP ta bari a asusun jihar.
Shugaban jam'iyyar na PDP ya ce, duk da wadannan kudade da jihar ta karba ba ta tsinana komai ga jihar ba.
Saidai, Abdu Labaran, mai bawa gwamna shawara a bangaren yada labarai ya yi watsi da wannan zargi na jam'iyyar PDP tare da bayyana cewar jihar ba ta batar da ko sisi ba ta hanyar da bai dace ba.
Labaran ya kara da cewa tuni jam'iyyar PDP ta mutu a jihar Katsina amma mutane irinsu Maigari sun kasa gane hakan.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng