Yanzu Yanzu: Mutane 3 sun mutu a harin kunar bakin wake na sabon shekara da aka kai garin Adamawa
Mazauna wani gari uku a karamar hukumar Madagali dake Adamawa sun rasa rayukansu sakamakon wani harin bam da aka kai a ranar Litinin, 1 ga watan Janairu, a cewar wami rahoto daga kamfanin dillanci labarai na Najeriya (NAN).
Rahoton ya kawo cewa an dasa bam din ne a wani hanya dake garin sannan kuma cewa Othman Abubakar, Kakakin yan sandan jihar Adamawa, ya tabbatar da al’amarin amma ya ce mutun daya kawai aka kashe.
Abubakar ya kara da cewa hukumar na ci gaba da tattara bayanai domin cikakkaen rahoto.
Rahoton ya kara da cewa babban sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Adamawa (ADSEMA), Mista Haruna Furo, ya tabbatar da al’arin.”
KU KARANTA KUMA: Gwamna Bindow ya yafewa fursunoni 37 a Adamawa
“Na amsa kira daga shugaban karamar hukumar Madagali game da al’amarin amma saboda rashin kyan kafar sadarwa hiran namu ya yanke.
“Nayi kokarin sake kiransa lokuta da dama amma hakan bai samu ba,” Inji Furo inda ya kara da cewa har yanzu hukumar bata samu cikakken bayani kan harin ba.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng