Hotuna: Sojan Najeriya ya yi bikin murnar cika shekaru hudu a raye yana yaki da Boko Haram a jihar Borno

Hotuna: Sojan Najeriya ya yi bikin murnar cika shekaru hudu a raye yana yaki da Boko Haram a jihar Borno

- Sojan Najeriya ya yi murnar cika shekaru hudu a filin daagar yaki da Boko Haram a jihar Borno

- Sojan ya yi bikin da abokan aikinsa sojoji a can jihar Borno

- Ya ce wannan shine karo na hudu yana murnar zagayowar ranar haihuwar sa a filin daagar yakin

Wani Sojan Najeriya, Ochi Frank, ya yi murnar zagayowar ranar haihuwar sa karo na hudu a filin daagar yaki a jihar Borno.

Hotuna: Sojan Najeriya ya yi bikin murnar cika shekaru hudu a raye yana yaki da Boko Haram a jihar Borno
Sojan Najeriya ya yi bikin murnar cika shekaru hudu a raye yana yaki da Boko Haram a jihar Borno

Frank ya bayyana cewar wannan shine karo na hudu yana murnar zagayowar ranar haihuwar sa a jihar Borno. Ma'ana ya shafe tsawon shekaru hudu kenan a jihar yana yaki da 'yan kungiyar Boko Haram.

Hotuna: Sojan Najeriya ya yi bikin murnar cika shekaru hudu a raye yana yaki da Boko Haram a jihar Borno
Sojan Najeriya ya yi bikin murnar cika shekaru hudu a raye yana yaki da Boko Haram a jihar Borno

A cewar Frank ya yi murnar zagayowar ranar haihuwar ta sa da abokan aikinsa, kuma sun yi shagalinsu da iya abubuwan makulashe da zasu iya samu a wurin da suke aiki.

DUBA WANNAN: Gudaddun 'yan Boko Haram sun kaiwa sojoji hari a jihar Yobe

"Wannan shine karo na hudu ina bikin murnar zagayowar ranar haihuwata a cikin Sahara. Ba iya murnar zagayowar ranar haihuwata nake yi ba, ina murnar cika shekaru hudu da rai, ina yaki da 'yan Boko Haram. Sannan ina Murnar zan bar filin daagar yaki da raina domin da yawa basu samu wannan damar ba," a cewar Frank.

Hotuna: Sojan Najeriya ya yi bikin murnar cika shekaru hudu a raye yana yaki da Boko Haram a jihar Borno
Sojan Najeriya ya yi bikin murnar cika shekaru hudu a raye yana yaki da Boko Haram a jihar Borno

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: