Sojojin Najeriya sun dare saman fitaccen dutsen ‘Aso Rock’ sun yi atisaye

Sojojin Najeriya sun dare saman fitaccen dutsen ‘Aso Rock’ sun yi atisaye

- Sojojin Najeriya sun dare saman dutsen nan na ‘Aso Rock’ jiya

- Shugaban Sojin Kasar yana cikin wadanda su kayi wannan aiki

- Barikin Rundunar Sojin kasar ta kare ayyukan ta na shekarar nan

Rundunar Sojin kasar nan da ke kula da kan iyakar Birnin Tarayya Abuja sun kare ayyukan bana da hawa saman dutsen nan da aka sani watau na ‘Aso’. Sojojin sun yi hakan ne don motsa jikin su.

Sojojin Najeriya sun dare saman fitaccen dutsen ‘Aso Rock’ sun yi atisaye
Rundunar Sojojin Najeriya a kololuwar saman Aso Rock

A cikin Rundunar da tayi tattaki zuwa saman wannan dutse akwai Shugaban Hafsun Sojin Kasar Laftana Janar Tukur Buratai. Shugaban Bataliyan Sojin da ke gadin Garin Shugaban Kasa Manjo Janr MS Yusuf mai shirin barin gado ne ya gayyaci Janar Buratai.

KU KARANTA: Za a fara damke masu yin waya a gidajen man fetur

Sojojin Najeriya sun dare saman fitaccen dutsen ‘Aso Rock’ sun yi atisaye
Sojojin Najeriya tare da Janar MS Yusuf a gaba

Kamar yadda Mai magana da yawun Sojin kasar ya bayyana Birgediya Janar SK Usman, daga cikin wadanda su ka hau dutsen akwai wadanda ba Sojojin Kasa ba ba irin su Jami’an kula da hanyoyin kasa watau FRSC da kuma Sojin sama da na ruwa na Kasar.

Dutsen dai yana da tsananin tsawo na akalla taku 34, 000 daga kasa kuma wannan ne karo na farko da Shugaban Hafsun Soji zai ja tawagar sa zuwa saman dutsen a tarihin Najeriya inji Birgediya Janar Sani Kukasheka Usman na Rudunar Sojin Kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng