Cab-di-jan: Namiji ya haihu bayan wata mata tayi masa ciki
- Wani Mutumi da ya zama mace ya dauki ciki har ya haihu
- Wata Mata ce wanda a da namiji ne yayi masa ciki a bana
- Yanzu haka an samu yaro sanbalele har yayi makonni 16
Kwanan nan mu ka samu wani labari mai ban mamaki daga Jaridar Daily Mail ta Turai inda wani Mutumi mai suna Diane Rodriguez ta haifi yaro bayan wata Mata Fernando Machado tayi masa ciki a can kasar waje.
Abin da ya faru dai a hakika shi ne Fernando Machado asalin ta mace ce wanda ya koma namiji daga baya. Ita kuma Diane Rodriguez, asalin ta namiji ne aka yi wa aiki a asiniti ta zama mace. A haka ne su ka tara har aka samu karuwa.
KU KARANTA: 'Yan adawa sun sa Yaron Shugaba Buhari a addu'a bayan yayi hadari
Ba a taba samun dai irin wannan iyali ba a Duniya. Machado na zaune da iyalin na su a Kasar Ecuador kuma tayi wa Matar ta cikin ne a Kasar Afrika ta Kudu kwanakin baya. Yanzu haka jariri ya fara girma har ya kai watanni 4 a Duniya.
Bayin Allan dai sun ce ba su radawa yaron suna ba har yau ko da dai ana kiran sa Caraote (Ma’anar sunan shi ne dodon-kodi). Rodriguez da asalin ta namiji ne mai suna Luis kamar Mijin ta, ta sauya halittar ta inda shi kuma a da mace ce.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng