Takaitaccen tarihin rayuwar Marigayi Alhaji Musa Dankwairo

Takaitaccen tarihin rayuwar Marigayi Alhaji Musa Dankwairo

Marigayi Alhaji Musa Dankwairo zai ci gaba da kasancewa daya daga cikin mawakan da darajarsu a idon duniya take kara habaka a al'ummar hausawa, sai dai girmamawar bata tsaya iyaka nan ba domin kuwa manazarta a duniya suna ci gaba da amfanuwa da gudunmawar da ya baiwa fagen ilimi, musamman farfesoshi da masu binciken ilimi akan Yaren Hausa dake nazari a jami'o'in Najeriya da kuma gabannan.

Wani malami na jami'ar Usmanu Danfodio dake Sokoto, Farfesa A.M Bunza ya bayyana cewa, an haifi marigayi ne a shekarar 1907, a garin Bakura wanda ke tsakanin jihar Zamfara da Sokoto da kimanin kilomita 105.

Sunan Mahaifinsa Usman Dankwanda, ya rayu a garin Kaya dake karkashin karamar hukumar Maradun, inda yake yiwa Sarkin Kayan Maradun waka a fadar sa. Mahaifin Dankwairo da kakansa duk makadan Sarkin Kayan Maradunne. Ya tashi ya tarar da kakansa da kahaifinsa suna waka tare, amma ya fi rayuwa da mahaifinsa rayuwa ta hakika, kuma tun yana dan shekaru 6 zuwa 7 ya fara fita inda mahaifinsa ke zuwa da shi cikin tsangaya ta waka.

Bayan rasuwar mahaifinsa, sai ragamar kungiyar waka ta koma hannun Aliyu Kurna, wanda wa ne ga Dankwairo, inda aka zabi Dankwairo ya zamto mataimakin Aliyu, wanda ida bayanan sai Dankwairo ya wakilce shi a matsayin shugaban tawaga.

Marigayi Alhaji Musa Dankwairo a lokacin yana matashi da kuma dattijo
Marigayi Alhaji Musa Dankwairo a lokacin yana matashi da kuma dattijo

Marigayi Alhaji Musa ya samu wannan lakabi na 'Dankwairo' tun lokacin mahaifinsa na raye. Mahaifinsa ya na da wani Yaro da ake kira Dankwairo saboda zakin muryarsa da kuma kwarewa wajen yin wake, sai Musa ya rinka kwaikwayon sa tare da kwaikwayon muryarsa. Ganin cewa Musa ya kware kamar shi Dankwairon na asali sai ake kiransa da wannan lakabi na Dankwairo.

Tun daga wannan lokaci Dankwairo ya fara shahara a fagen waka, wanda hakan ya sanya ya zamto mawaki ga marigayi Sardaunan Sokoto, Alhaji Ahmadu Bello, inda Dankwairo ya rera masa wakarsa ta farko da takenta na 'Mai Dubun Nasara Garnaki Sardauna'.

Marigayi Sardauna ya fifita tawagar Dankwairo fiye da kowace kungiyar waka, inda ya maishe da Dankwairo mawakin fadar sa tare da kyautatawa ta wuce misali wadda a wancan lokaci hankali baya kaiwa ga irin kyaututtukan da Sardauna ya rinka yiwa Dankwairo da 'yan tawagarsa, kama daga suturu zuwa motar hawa.

KARANTA KUMA: Kururuwa ta biyo bayan ci gaba da takkadamar shugabannin hidima na Najeriya

A takaice dai, Musa Dankwairo ya yiwa Sardauna wakoki guda 17, kuma musabbabin saduwarsa da Sardauna kuwa a fagen siyasar NPC (Nothern People's Congress) ne suka hadu, kasancewar Sardauna dan Siyasa kuma Basarake, saboda haka yana bukatar mawakin sarauta da zai zauna tare da shi a fadarsa domin dabbaka sunan sa.

Bayan rasuwar Sardauna a shekarar 1966, tawagar Dankwairo ta kwanta dama har na wani lokaci mai tsawo kafin ta ci gaba da wakokin yabo ga wasu sarakunan gargajiyar a suka shahara irin su; Sarkin Daura Bashar, Sultan na Sokoto da Sarkin Zazzau Aminu.

Cikin shekaru 29 zuwa 30 da suka gabata, wa'adi na rayuwa ya riski marigayi Dankwairo, inda ya bar 'ya'ya 14, maza 7 da mata 7, tare da jikoki 104 a yayin muturwarsa, wanda sun ci gaba da hayayyafa kamar yadda babban dan sa; Alhaji Garba Musa Dankwairo ya bayyana.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel