Direban da ya tsinci kudi da gwala-gwalai a motar sa ya maidawa mai shi
- Wani Direba ya nuna cewa akwai na-kwarai har yanzu a Duniya
- Wata Mata ta manta da jakar ta dauke da Dukiyar ta a motar sa
- Duk da halin da ake ciki wannan Direba bai yi gaba da kayan ba
A makon jiya ne kamar yadda mu ka samu labari wani Bawan Allah yayi abin da ba kowa zai iya ba inda ya maidowa wata mata kayan ta da ta bari a motar sa dauke da makudan dukiya a ciki. Oodua ce ta kawo wannan labari kwanakin baya.
Dama an ce ko ina ba a rasa na kwarai kuma an yi haka, Farfesa Margaret Olabisi Araoye ta bayyana yadda Direban da ya dauko ta daga tasha a Abuja ya maido mata da jakar ta har dakin da ta sauka bayan tayi mantuwa.
KU KARANTA: An jefa wadanda su ka saci waya a gidan kurkuku
Abin da zai ba ka mamaki shi ne dai a cikin jakar akwai na’urar Komfuta karama da kuma ‘yan kunnen gwa, da fasfon fita kasar waje da kuma sauran abubuwa irin su katin ATM da lasisin tuki. Ban da kuma kudi har N50, 000.
Direban ya duba jakar wannan mata ne inda ya samu lambar mijin ta wanda bayan nan ne aka dace da kiran wannan mata. Wannan Direba dai Bahaushe ne mai suna Abubakar Hassan.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng