Sergio Ramos ne ya fi kowa shan jan kati a La-liga
– Sergio Ramos ya shiga cikin littafin tarihin Kasar Sifen
– ‘Dan bayan dai ya ajiye wani mummunan tarihi a kwallo
– Sau 24 ana ba Sergio Ramos jan kati a wasan kwallon kafa
Labari ya kai gare mu cewa Duniya ta sallamawa Sergio Ramos a wajen wani abin da ba a so bayan da Dan wasan na Real Madrid ya kafa wani mummunan tarihi a karshen makon nan. Sau 24 kenan ana ba Sergio Ramos jan kati a rayuwar sa.
Dan wasan bayan Real Madrid Sergio Ramos ne ya fi kowa shan jan kati a Gasar Kasar Sifen watau La-liga. A wasan Madrid da Athletic Bilbao na wannan makon ne Ramos ya sha jan katin sa na 19 a La-liga wanda ya sa ya buge kowa a tarihi.
KU KARANTA: Ana rikicin tsakanin Sojoji da masu yi wa kasa hidima?
Ramos ya karbi katin ne daf da za a tashi wasa, dama can Alkalin wasa ya gargade sa bayan sun yi arangama da Raul Garcia a minti na 11 kafin ya kuma hade da ‘Dan wasa Aritz Aduriz a karshen wasan. Real ta tashi wasan ne babu ci wannan karo.
Sergio Ramos na Real Madrid yanzu ya sha gaban ‘Yan wasa irin su Pablo Alfaro da Xavi Aguado da su ka taba karbar jan kati sau 18 a rayuwar su . Ba mamaki nan gaba ma dai ‘Dan wasan ya karbi wasu jan katin. Yanzu Ramos ba zai buga wasan Madrid da Sevilla ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng