Raba kasar Najeriya ba shi bane mafita - Inji babban Bishof
- Limamin darikar Angilika ta Kiristoci yayi kira ga 'Yan kasa
- Rabaren Ali Lamido yace a guji kiran a raba Kasar Najeriya
- Dr. Lamido ya kuma yi kira ga Gwamnatin kasar kan tsaro
Wani babban Malami na Addinin Kirista da ke Arewacin Najeriya yayi kira da hadin kai a Kasar a wani huduba da yayi a coci a wannan makon.
Bishof Dr. Ali Buba Lamido ya gargadi masu kukan a raba Najeriya inda yace ba hakan ne zai kawo mafita na matsololin kasar ba. Babban Limamin na cocin Wusasa da ke Garin Zariya yayi wannan kira a hudubar sa ta wannan makon a Garin na Zariya.
KU KARANTA: Atiku ya fice daga Jam'iyyar APC zuwa PDP
Rabaren din yace raba kasar Najeriya ba shi bane zai fitar da kasar daga halin da aka shiga inda yace idan babu hadin kai ko kashi 100 aka raba Najeriya ba za a taba samun hadin kai ba. Malamin ya kuma yi tir sa masu raba kan jama'a da sunan addini a Kasar.
Dr. Ali Lamido yayi kira da Jama'a su guji kabilanci da nuna bambancin addini a lamarin su. A karshe Limamin na cocin Angilika yayi kira ga Gwamnati da su kare rayukan jama'a tare da kawo karshen rikice-rikice irin na Makiyaya a fadin Kasar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng