2019: Su waye dattijan Arewa, kuma wacce rawa suke takawa wajen ci gaban arewar?
- Arewa na da manya da sarakuna na gargajiya, amma har yazu tafi kowanne yanki matsala
- Sai lokutan zabe akan ji wadannan dattijai suna kankamba kan waye za'a zaba
- Baka jinsu a lokutan yunwa, ko tabarbarewar tsaro, ko matsalolin almajirci a arewar
A lokuta da dama a arewa, idan kana yawo a titi, zaka dauka yanki ne da bashi da dattijai, babu iyaye, inda zaka sami almajirai mata da yara kanana, suna bara da kwano a hannu, babu wanda ya damu da ina iyayensu.
A arewa ne, ake samun fadace-fadace na kabilanci, da na addinanci, tsakanin kirista da musulmi, da kuma tsakanin musulman kansu, kawai don wani dan shi'a ne ko dan izala ko ma dan darika, sai a far masa a kashe shi, kuma makota da abokai kan iya nuna shi ma ga makasansa.
A arewa ne kadai, a duk fadin kasashen musulmi na duniya, mutum zai yi aure, yayi cikinsa, ya haifi yaro, amma ya wullar da yaron nan tun yana dan karami, wai shi bazai ciyar da tarbiyyantar da dan ba, ba zai sanya mishi tufafi ba, ba kuma zai kaishi makaranta ba, sai ya jea wa jama'a wai su ciyar masa dashi, domin shi mai koyon karatun Kur'ani ne.
DUBA WANNAN: An so yi wa Aliko Dangote fashi amma jami'an tsaro sun dakile harin
Sai an karato lokutan zabe, ko wani rabon arziki na kasa, kwatsam, daga wannan yanki, sai kaji wasu su zumudi, sun fito da sunan wai su iyaye ne, wai su dattijai ne, wai su suke kare hakkokin jama'ar su, wai sun san jiya sun san yau, wai su suke fadin yadda za'a yi.
Zaka jisu da kungiyoyi kamar su Arewa Consultative Forum, Arewa Youth Forum, Northern Elders Forum da sauransu.
Sun kasa taimakon yankin wajen hada kansu domin ciyar da talakka gaba, amma sai neman matsayi da siyasa da kakabe suka sanya a gaba, wai su hadu tsakar dare su ce zasu zaba ma Najeriya shugaba, ko wai sun ari bakin mu jama'ar arewa, domin su tauna mana albasa.
Tirr da halin mu na ko-in-kula!
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng