Ya kamata Najeriya ta daina wadannan bidi’a – Aisha ta caccaki gwamnatin tarayya saboda kaddamar da hutu
- Aisha Yesufu bata ji dadin kaddamar da ranar Juma’a 1 ga watan Disamba a matsayin ranar hutu da gwamnatin tarayya tayi ba
- A cewar ta, hutu ne mara amfani sannan kuma akwai bukatar Najeriya ta dakatar da abun da ta kira da “gasar addini”
- Yayinda mutane da dama suka goyi bayan ta, wasu sun bukaci ta daina korafi
Daya daga cikin jagoran kungiyar masu neman a dawo da yan matan da aka sace (Bring Back Our Girls group), Aisha Yesufu ta yi Allah wadai da hutun da gwamnatin tarayya ta kaddamar don raya ranar maulidi.
Da take bayyana hutun a matsayin bata lokaci, ta nemi sani yaushe Najeriya ta fara bikin Maulidi.
Aisha tace akwai bukatar Najeriya su maida hankali wajen yin abunda zai amfani mutane maimakon kasancewa cikin “gasar addini”.
A cewar ta, hutun Maulidi na farko da aka fara a Najeriya shine wanda ministan cikin gida, Godwin Abbe, karkashin gwamnatin marigayi ya kaddamar a ranar Litinin, 9 ga watan Maris, 2009.
Yayinda mutane da dama suka goyi bayan ta, wasu sun bukaci ta daina korafi.
KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa bai kamata Buhari yayi zancen dawowa na biyu ba a yanzu – Sage Africa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng