Wannan motar limousine na N720m na tafiya a kan titi da kuma ruwa (hotuna)
An kera wani sabon mota wanda ya hada tsada da kuma tsantsar kyawu mai ban mammaki.
Abun ban mamaki game da motar shine yana iya tafiya akan titi da kuma ruwa. Motar ya kan kasance kirar Limousine idan yana tafiya kan titi sannan kuma ya zamo jirgin ruwa kan ruwa.
Motar kirar Limousine ne sannan kuma farashin motar ya kai kimanin naira miliyan 720 (Dala miliyan 2).
Ya na iya daukar fasinjoji 12 da kuma matuka guda biyu. Yana kuma da bandaki a ciki.
Motar ya kasance daya daga cikin mafi tsada a kasuwar yau.
Ga karin hotuna a kasa:
KU KARANTA KUMA: Tsohon gwamna Bafarawa yayi watsi da hotunan neman zaben shugabancin kasa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng