Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure

Basa bam ba, duk da irin cece kuce, ji ma juna ciwo, tare da rasa rayuka da aka sassamu a yan kwanakin nan, duk a sakamakon rikici a tsakanin ma’aurata, an samu wata mata da ta yi alwashin biya ma mijinta sadaki don ya karo mata.

Jaridar Rariya ne ta sha hira da wannan mata a ranar Juma’a 24 ga watan Nuwamba, inda matar ta bayyana sunanta da suna Hajiya Saratu Arbi Kamba, wanda ta ce tana goyon bayan mijinta ya kara mata.

KU KARANTA: Daki-daki yadda Atiku ya dinga sauyin sheka a tsakanin jam’iyyun Najeriya

Saratu ta ce abokiyar zama baa bin gudu bace, inda ta ce a lokacin da mijinta ta, Alhaji Arbi Kamba, ta bayyana cewa ita da kanta ta sanya albarka a auren da mijinta zai karo, bayan ya shaida mata niyyarsa.

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure

Hjaiya Saratu

Da majiyar Legit.ng ta tambayi Hajiya Saratu ko bata gudun amarya ta kwace mata miji, sai tace ta yarda da soyayyar da mijinta ke yi mata, dojn haka bata kawo wannan batu zuciyarta.

Saratu ta ce kafin auren mijin nata, ta samu shawarwari irin na ingiza mai kan turuwa daga yan uwan ta mata, amma duk ta yi watsi da batutuwansu, har ma ta yi alkawarin bada tata gudunmuwar ga auren, ta hanyar biya masa sadakin aure.

Daga karshe ta ja hankalin mata dasu tuna cewa mata hudu aka bukaci namiji ya aura matukar zai iya adalci, don haka ya kamata su sani kishiya abokiyar zama ce, ba abin gudu ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel