Likafa ta ci gaba: Malaman ƙungiyar Izala sun tsallaka nahiyar Turai don aikin Da’awah
- Shuwagabannin kungiyar Izala sun tsallaka nahiyar Turai domin Da'awah
- Daga cikin Malaman sun hada da Sheikh Bala Lau da Sheikh Kabiru Gombe
A kokarinta na cigaba da watsa sakon addinin Musulunci lunguna lunguna na kasar nan kamar yadda ta saba, a yanzu ma kungiyar Izalatil Bidi’ah wa iqamatissunnah, JIBWIS ta samu cigaba.
Wasu daga cikin Malaman kungiyar sun tsallaha nahiyar Turai don gudanar da aikin watsa addinin Musulunci a kasashen dake wannan yankin, ta hanyar yin Da’awar addinin.
KU KARANTA: Kare ya ciji gaban wani Mutumi a lokacin da yayi ƙoƙarin zakke ma wasu Mata ƙanana
Rariya ta ruwaito daga cikin Malaman akwai shugaban kungiya, Sheikh Bala Lau, tare da sakataren kungiyar Sheikh Kabiru Gombe.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito daya daga cikin hadiman shuwagabannin kungiyar, Mal Musa Isah ne ya raka zuwa filin sauka da tashin jirage, yayin da suke kan hanya.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng