Kaicho! Dattijo dan shekara 80 ya nakada wa uwarsa mai shekaru 100 duka har lahira

Kaicho! Dattijo dan shekara 80 ya nakada wa uwarsa mai shekaru 100 duka har lahira

- Wannan al'amari ya faru ne a Marke Gada Maje, na Jihar Neja

- Mutumin ha kashe mahaifiyar ta sa ne bisa zargin ta kashe mashi jika ta hanyar maita

- Ya ce daman ya san mahaifiyar ta sa mayya ce, kuma jikar ta sa ta yi ta ihu kafin ta mutu, ta na rokon mahaifiyar ta sa ta sakan mata kurwarta

Wani mutum mai shekaru 80, Kwacha Manu, tare da dan sa mai shekaru 40, Likita, sun shiga hannun hukumar 'yan sanda ta Jihar Neja bisa laifin zane mahafiyar Manu, Inne kayyo, kuma kaka ga Likita, mai shekaru 100, har sai da ta mutu. Wannan lamari ya faru ne a Marke Gada Maje na Jihar.

Inne kayyo ta riski ajalin ta a hannun dan ta ne sakamakon zargin ta ya yi na kashe Magajiya, 'yar Likita, mai shekaru 17, ta hanyar maita. A nan ne fa dan nata, Manu, ya dauki sanda ya dinga labta mata har sai da ta mutu

Kaicho! Dattijo dan shekara 80 ya nakada wa uwarsa mai shekaru 100 duka har lahira
Kaicho! Dattijo dan shekara 80 ya nakada wa uwarsa mai shekaru 100 duka har lahira

Wata majiya ta ce daman Inne ta saba kashe zuri'ar ta ta hanyar maita, Magajiya ita ce mutum ta 9 da ta mutu ta wanann hanya. Shi kuwa Manu da ya amsa laifin sa, ya ce a kafa ne ya bugi mahaifiyar ta sa, bugun da bai isa ya kashe ta ba.

DUBA WANNAN: Kalli hotunan irin tarbar da Gwamnoni da masu sarautun gargajiya sukayi wa Buhari a Enugu

Ya kuma ce kashe mashi jikanya da ta yi ne ya ga ba zai iya kyale ta ba tare da ta dandana kudan ta ba. Da a ka tambaye shi yadda ya tabbar Inne ce ta kashe ta, sai ya ce Magajiya kafin ta rasuwa, ta yi ta ihu ta na rokon Inne da ta sakan mata kurwarta.

Ya kuma ce daman ya san mahaifiyar ta sa mayya ce. Shi kuwa Likita ya ce bai san dalilin kama shi da 'yan sanda su ka yi ba, don kuwa ba ma ya garin lokacin da al'amarin ya faru. Hukumar 'yan sanda kuwa ita cewa ta yi, sun amsa laifin su kuma za a gurfanar da su gaban kotu.

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164