Tun yana Makaranta Buhari mutum ne mai natsuwa kuma bai taba cin bashi ba – Inji wata tsohuwa
-Wata tsohuwa ta bayyana halin Buhari lokacin yana Makaranta
- Tsohuwar tace Buhari da Gowon su na zuwan shan kunu wajen ta
- Sai dai tace Buhari bai taba karbar bashi ba kamar sauran Sojoji
Labari ya zo mana daga Jaridar Punch inda wata tsohuwa ta bayyana wanene Shugaba Buhari tun yana matashi ‘dan Makaranta a Kaduna tare da irin su Janar Yakubu Gowon
Wata Dattijuwa mai suna Ochefu wanda ta fara kafa shagon ‘Mammy’ a Makarantar Sojoji tace ta san Muhammadu Buhari tun yana Makarantar inda tace mutum ne mara son rikici da hayaniya tun asalin sa tana cewa mutum ne kuma mai saukin kai.
KU KARANTA: Yadda aka daure Marigayi Sardaunan Sokoto Ahmadu Bello
Tsohuwar tace a lokacin su na Makarantar Soji ta NDA kullum za ka ga Shugaba Buhari tsaf-tsaf cikin tufafin sa. Wannan tsohuwa tace lokacin tana saida kunu, Sojoji kan sha ne a kan bashi, amma Buhari a-nan-take yake biyan ta ba tare da jiran albashi ba .
Wannan mata Madam Ochefu tace a lokacin da aka maida Mijin ta aiki Legas, Muhammadu Buhari ya shaku da wani karamin yaron ta Yakubu wanda yanzu haka ya zama Farfesa a kasar nan.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng