Wasiyyar Saddam Hussein ga al’ummar Musulmai

Wasiyyar Saddam Hussein ga al’ummar Musulmai

- Gabanin a dau ransa ta hanyar rataya, marigayi Saddam Hussain ya bar wa al'ummar Musulmai wasiyya

- Marigayi Saddam ya ce ya yi gwagwarmaya da makiya Islama domin tabbatar da tsaro a kasar Iraki

- Tsohon shugaban ya zargi shugabannin kasashen Musulmai da kula makirci da azzaluman kasashen yamma

Gabanin a dau ransa ta hanyar rataya, tsohon shugaban kasar Iraki, marigayi Saddam Hussein ya bar wa al'ummar Musulmai duniya wasiyya kamar haka:

"Da sunan Allah mai rahama mai jin kai.Dukkan yabo ya tabbata ga cikamakin mazanni, Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da ahlinsa.Allah ne shaidana, a tsawon rayuwata na yi gwagwarmaya da makiya Islama domin tabbatar da tsaro a kasata Iraki. Da yawa daga cikin ku sun butulce mun, inda a yanzu suke murnar mutuwata. Amma lokaci zai zo da za kuyi nadamar rashina. Ku kuma shugabannin kasashen Musulmai, kun bada ni hadaya ga azzaluman kasashen yamma, wadanda ke ci gaba kashe dubban Musulmai domin tabbatar manufarsu ta mallakar duniya. To ku sani cewa, ko ba dade, ko ba jima,zaku zama ababen farauta ga wadanda kuka mara wa baya a yau. Wasu daga cikinku na kokarin kawo mun tallafi, amma su daina. Domin na mika rayuwata ga ubangijina. Sai ku yi kokarin ceto na ku rayukan da kuma hana rabuwar kasar Iraki. Ya ku'yan uwana Musulmai na duniya, ku gaggauta hada kawunanku, ko kuma ku zama tamkar kwallo a hannayen Amurka da kawayenta. Allahu Akbar ! Allahu Akbar ! Babu wani abin bauta sai Allah, kuma Annabi Muhammadu Manzonsa".

Wannan ne wasiyyar karshe na tsohon shugaban kasar Iraki gabanin a dau ransa.

Wasiyyar Saddam Hussein ga al’ummar Musulmai
Tsohon shugaban kasar Iraki, Saddam Hussein

Marigayi Saddam Hussein ya kasance shugaban kasar Iraki daga Yuli 16, 1979 har zuwa 9 ga watan Afrilun 2003.

KU KARANTA: Buhari ya nuna damuwar sa akan taimakon da yan kungiyar Boko Haram suke samu daga kungiyar yan ta’adar ISIS

Idan baku manta ba a shekara ta 2003, hadin gwiwar wanda Amurka ta jagoranta ta kai hari Iraki don soke Saddam, wanda shugaban kasar Amurka na wacen lokacin, George W. Bush da firaministan Birtaniya, Tony Blair sun zarge shi da cewa ya mallaki makamai kare dangi da kuma goyon bayan kungiyar al-Qaeda.

Bayan da aka kama Saddam a ranar 13 ga watan Disamban shekarar 2003, an yi shari'ar tsohon shugaban a karkashin gwamnatin wucin gadi na Iraki. A ranar 5 ga watan Nuwamba 2006 ne aka zargi Saddam da laifuffukan kisan kiyashi wanda aka ce ya aikata a shekara ta 1982 yayin da kimani 'yan Shi'a Iraki 148 aka kashe, kuma aka yanke masa hukumcin kisa. An aiwatar da hukuncinsa a ranar 30 Disamba 2006.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng