Babbar matsalar masana'antar shirya fina-finai ta kannywood - Farfesa Abdallah Uba Adamu
- Matsalar masana'antar shirya fina-finai ta kannywood ita ce maimaita tsirarun jarumai cikin fina-finai
- Ya ce wannan halayya ta masu shirya fina-finan hausa ta sabawa tsarin shirya fina-finai na kasashen da suka ci gaba
- Masu shirya fina-finan musamman fardusoshi na da ra'ayin cewa ba kasafai fina-finai suke yin kasuwa ba idan masu kallo suka ga sabuwar fuska a cikin shirin
Wani farfesa mai koyar da darasin tsara fina-finan hausa a jami'ar Bayero dake Kano ya ce babbar matsalar masana'antar shirya fina-finai ta kannywood ita ce maimaita tsirarun jarumai cikin fina-finai. Farfesan ya ce matukar ba a bawa sabbin jarumai damar gwada basiararsu, ta yaya suma zasu shahara.
Farfesa Abdallah ya ce wannan halayya ta masu shirya fina-finan hausa ta sabawa tsarin shirya fina-finai na kasashen da suka ci gaba. Ya kara da cewa mai yiwuwa dalilin da yasa tsirarun jaruman mamaye harkar shi ne akasari su ne ke shirya fina-finan da kansu.
DUBA WANNAN: An kori wasu sojoji 38 daga aiki
Masu shirya fina-finan musamman fardusoshi na da ra'ayin cewa ba kasafai fina-finai suke yin kasuwa ba idan masu kallo suka ga sabuwar fuska a cikin shirin.
Farfesa Abdallah wanda yanzu shi ne shugaban jami'ar karatu daga gida ta Najeriya ya ce jami'ar sa tana kokarin fara wani kwas a kan harkar shirya fina-finai domin bunkasa ilimin fannin shirin wasan Hausa.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng