Dandalin Kannywood: Kyawawan hotunan Nazir Ahmad da sabuwar matar sa
Labarin da muke samu daga majiyoyin mu da dama na nuni ne da cewa a gobe juma'a za'a fara bukukuwan shahararren mawakin nan na fina-finan Hausa da kuma sarauta watau Naziru Ahmad da amaryar sa Halima Aminu a Kano.
Haka kuma kamar dai yadda muka samu shine cewa za a dauki kimanin kwanaki biyu ana shagalin bikin a Kano inda kuma ake sa ran halartar jama'a da dama musamman ma masu ruwa da tsaki a masana'antar.
KU KARANTA: Kotu ta daure wani dan gudun hijira
Legit.ng dai ta samu cewa tun a ranar Juma'a 14 ga watan Yuli aka daura auren a masallacin Umar Bin Khaddab akan kudin sadaki Naira dubu dari 2 lakadan.
Shi dai wannan auren na Naziru da Halima duk da auren soyayya ne za'a iya cewa basu shirya masa ba don kuwa ba a lokacin suka tsara suyi auren ba amma kasantuwar za'ayi wa yayar amaryar aure sai kawai aka hada da nasu aka yi.
Za a yi walimar cin abincin dare a ranar Lahadi.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng