Zan tsaya takarar dan majalisa a 2019 – Lawal Ahmad
Shaharren jarumin Kannywood, Lawal Ahmad ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar dan majalisar wakilai mai wakiltar Bakori/Danja a zaben shekara ta 2019.
Jarumin ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da jaridar Premium a ranar Alhamis da ta gabata.
A cewarsa ya yanke hukunci tsayawa takarar ne saboda irin goyon bayan da ya ke samu daga mazabar shi. Ya ce duk da cewa a Kano ya ke da zama, yana yawaita ziyarar mazabar ta shi, inda yake haduwa da mutanen shi.
Ya ce ya samu kiraye-kiraye da dama daga wajen su domin ya dawo gida ya yi takara.
A cewar Ahmad “Ina jin dadin taimakawa jama’a, kuma na yi wa jaha ta da mutane na abubuwa da dama da ba zan iya bayyana wa ba a nan."
Da aka tambaye shi ko ya na tunanin zai iya buge dan majalisa mai ci, Ahmad ya ce ya barwa Allah wannan. Shi dai ya san zai yi takara kuma zai samu goyon baya daga wajen mutanen shi, wanda hakan ne ke bashi karfin gwiwar zai samu nasara.
Yayin da 2019 ke karatowa, jarumin ya ce ya fara shirye shirye da tawagar shi, yayin da ye ke amfani da damar wajen fahimtar abubuwan da siyasa ta kunsa.
A cewar shi ”Na yi imanin zan yi nasara”.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng