Zancen banza kake yi: Wike ya caccaki Lai Mohammed
- Gwamnan Jihar Rivers Wike Nyesom ya ce Ministan yada Labarai, Lai Muhammed zan cen banza yake yi
- Ya bukaci a takawa Ministan birki kan yadda maganganun sa ke ruruta wutan rashin zaman lafiya
- Gwmanan ya kuma bayyana yadda rashin kawo canjin da zai amfani talaka ke iya kawo rashin zaman lafiya
Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike ya ce Najeriya ta na cikin hargitsi ne sakamakon gurbataccen shugabanci da danniya da wariya da kuma fifita 'yan uwa da abokai. Ya ce wadannan su ke kawo wargaza kasan.
Gwamnan ya kuma nemi a taka wa Ministan yada labarai, Lai Muhammed, birki kan maganganun banza da yake yi akan 'yan jam'iyyar adawa wanda hakan ke ruruta wutan rashin zaman lafiya da rarrabuwan kai a kasar.
Gwamnan ya fadi haka ne ga manema labarai a Fatakwal. ''Dole ne 'yan jarida su yi bincike sanan kuma su tona duk wani mai mugun nufi cikin 'yan adawa da ke kirkiran labarai yana yadawa don yi wa kokarin mu na ciyar da kasan nan gaba zagon kasa''. In ji Gwamnan.
DUBA WANNAN: Baiwa daga Allah: Matashi a Kano ya kera karamin jirgin ruwa (Hotuna)
Gwamnan kuma ya bayyana cewa al'ummar kasa bata taba yin kiran a sauya tsarin shugabanci da zai amfane ta ba kaman irin na wannan lokaci. Ya kuma ce rashin amsa kiran hatsari ne ga hadin kai da zaman lafiyar kasar.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kana kana da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng