Kiwon lafiya: Dubi Jerin sunayen abinci da ba zai cika muku ciki ko kara maku kiba ba
Abincin ka dai bahaushe na cewa garkuwar ka. Abinci na taka muhimmiyar rawa ga jiki da lafiyar mutum. Cin abinci mai kyau da inganci na iya bawa jiki da lafiya kariya daga cututtuka da kalubalen lafiya
Kamun alkama(Oatmeal): Kofi daya na kamun alkama zai samar da jikin ka da sinadarin faiba(fibre) da jikin ka zai sarrafa a hankali tsawon wuni guda.
Miya: Ruwan miya, musamman miyar ganye, na iya cika ciki kuma baya dauke da sinadarai masu kara kiba saboda yawan ruwa da ke cikin ta.
Salad: Idan har kuna neman abincin da zaku ci ku cika cikin ku ba tare da tsoron yin kiba ba to ku ci salad musamman Wanda ba ai wa hade-hade da kayayyaki marasa alfanu ga lafiya ba.
Gyada: Dangin gyada na da yawa kuma suna dauke da maiko amma mai kyau, wanda baya illata jiki. Cin nau'in gyada ciki hannu daya a rana zai taimakawa jiki wajen fitar da wasu sinadarai da jikin ke bukata domin aiki yadda ya kamata.
Abokado(Avocado): Suna dauke da maiko amma cin kadan bashi da wata illa ga jiki. Mai cin abokado yana da kyau ya ke yawan cin ganye.
Kwai: Kana son karin kumallon safe da zai rike ka har rana ba tare da kaji yunwa ba? To ku karyar da dafaffen kwai musamman ga wadanda kiba ta yi wa yawa.
DUBA WANNAN: Budaddiyar wasika zuwa ga Abubakar Shekau na Boko Haram
Wake: Babu ko shakka wake na daga cikin abinci masu rike ciki. Karin kumallo da wake zai rike maka ciki ba tare da mutum yana yawan ciye ciye da zasu kara masa kira ba.
Kindirmo: Daga cikin amfanin shan madara shine rashin kara kiba duk da kasancewar akwai maiko cikin ta. Yana da kyau ya san adadin kitsen jikin sa kafin ya ke yawan shan kindirmo.
Gugguru: matukar ba cika shi da bota ko mai ba, cin gugguru ya fi karawa jiki lafiya a kan cin soyayyen dankali ko shan cakolati. Gugguru na kosarwa da cika ciki bayan samarwa da jiki karfi ba kuma tare da ya karawa jiki kiba ba.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng