Kannywood: Bosho ya karyata murya da ke yawo a gari kan kiran da Boko Haram wai suka yi masa, yace ba shi bane
Shararren dan wasan barkwancin hausa, Sulaiman Yahaya, da a ka fi sani da "Bosho" ya karyata cewar kungiyar boko haram ta kira shi a waya domin ya ke hada mata bama - bamai. Bosho ya ce " wallahi ba wani dan boko haram da ya taba kira na a waya. Ni ma ina zaune a ka zo min da Wata hira da a ka nada a matsayin "wai" ni ne nake magana da yan' kungiyar boko haram, har wai suna son nake hada masu bam. Munyi dariya sosai bayan mun saurari hirar domin mun dauki abin a matsayin raha. Abin da kawai banji dadin sa ba shine zagin, mai martaba sarkin kano, da a kayi cikin hirar."
Bosho ya ce hakan ta faru ne shekara biyu da ta wuce, yana mai bayyana cewar anyi hakan ne domin a bata masa suna amma sai gashi ya kara jawo masa daukaka.
DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ya baiwa Osinbajo babban maki
Bosho na wannan bayani ne cikin wani faifan bidiyo mai cike da barkwanci da shafin yada labarai na BBC ya wallafa a yanar gizo. Bosho ya ce, ya samo sunan "Bosho" ne tun daga makaranta, "Saboda karatu sai nayi kwana 15 banyi bacci ba, sai daga baya na biya bashin baccin". a fadin Sulaiman Bosho.
Bosho ya ce, sana'ar wasan kwaikwayon yanzu ta neman kudi ce kawai amma ba don daukaka al'ada ko tallafar addini ba.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng