Ayyuka 3 da su ka fi albashi a Duniya
- Aikin Likitanci ya fi kowane aiki kudi a kaf Duniya a yanzu haka
- Wadanda su ka karancin ilmin na'ura mai kwakwalwa su na sahun gaban
- Akwai kudin gaske a harkar tukun jirgin sama da na sarrafa magunguna
Tun ba yau ba dai Likitoci sun yi kaurin-suna musamman kuma wajen karbar albashi mai tsoka a Duniya. Haka kuma Ma'aikatan mai ba a bar su a baya ba.
1. Likita
Likita musamman na Mahaukata da kuma mai fyede maras lafiya na cikin wanda ya fi kowa albashi a Duniya.
2. Injiniyan man fetur
A wasu wuraren a Duniya masu Dirgiri a wannan fanni na samun alal akalla Dala 130,000 a kowace shekara. Akwai kudi a harkar man fetur.
KU KARANTA: Wata mata ta taimaki Mijin ta da jari
3. Na'ura mai kwakwalwa
Wadanda su ka karancin wannan ilmi su na cin karen su babbaka a Duniya don kuwa da su ake damawa yanzu.
Masu aikin tukin jirgin sama da kuma ilmin sarrafa magunguna ba a bar su a baya ba a magana da ake yi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Dalilin tashin farashin kaya
Asali: Legit.ng