Musa mai Sana’a ya nemi yafiyar Masarautar Kano
Shahararren jarumin nan da ya yi fice a harkar fim din barkwanci kuma daraktan shirya fina-finai, Musa Mai sanaá ya shirya wani fim mai suna “Masu”, fim din day a tara manyan jarumai, ciki harda Saratu Gidado da aka fi sani da Daso.
Sai dai wannan fim ya bar baya da kura, sakamakon tarin rigingimu da fim din ya haddasa.
Tun farkon fara fim din ake gamuwa da matsala har kawo yanzu da ya kuma gamuwa da wata matsalar.
Fim din ya taba mahibbar masarautar kano, sabida yin amfani da masu biyu da Darakta Musa Mai Sana’a ya yi.
Wanda hakan ya saba ma dokar fim saboda kudirinta na son kare aláddun Hausawa da masarauta.
KU KARANTA KUMA: Aisha Buhari za ta ziyarci jihar Imo a gobe Laraba
Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya nuna takaicinsa bisa wannan lamari.
Hakan ya sa Musa da Dasu suka nemi afuwar masarautar kan cewa ta yafe masu, sakamakon kuskure da sukayi gurin amfani da tagwayen masu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng