Dan kasuwa ya aurar da mata marayu da nakasassu 50 a jihar Yobe
- Wani Shahararren dan kasuwa a Jihar ya aurar da 'Yan mata marayu da marasa galihu akalla su 50
- An daura auren ne a kofar fadar mai martaba sarkin Bade
Wani Shahararren dan kasuwa a Jihar Yobe mai suna Alhaji Mohammed Yakubu Jacob ya aurar da 'Yan mata marayu da marasa galihu akalla su 50 a kofar fadar mai martaba Sarkin Bade, Alhaji Abubakar Umar Sulaiman.
Legit.ng ta samu labarin cewa wannan al' amarin ya dauki hankulan al'umma da dama kasantuwar cewa a cikin watan da ya gabata ma wannan bawan Allah ya aurar da 'Yan mata 40 a garin, bayan Iyaye da wasu wakilai sun kai kokensu a gare shi.
KU KARANTA KUMA: Wani dan Najeriya ya yi ma dan matarsa mugun duka saboda ya siyo masa biredi a maimakon sigari da ya aike sa (HOTUNA)
A cewar mai Martaba sarkin Bade, akasarin 'Yan matan marayu ne da 'Yan gudun hijira wadanda suka sami mazajen aure, amma Iyayen su ko wakilan su ba su da halin aurar da su sakamakon halin rashi.
KU KARANTA KUMA: Kyamar Musulmai ya janyo an kashe mutane 2 a Amurka
A yanzu haka dai wannan bawan Allah ya koyar da 'Yan matan sana'o'i daban-daban tare da basu jari domin dogaro da kai, sannan Fadar sarkin ta nada wani kwamiti da zai dinga yin sulhu a tsakanin ma'auratan dan samun kyakkyawar fahimta a rayuwarsu ta aure.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Kalli wannan bidiyo na Legit.ng kan wanda ya kamata a kama tsakanin dalibai, malamai ko kuma iyaye idan yara sukayi satar jarrabawa
Asali: Legit.ng