Fada ya kacame tsakanin kasar Koriya ta Arewa da Amurka
- Rahotanni sun bayyana cewa Koriya ta Arewa ta gargadi Amurka da cewa a shirye take ta kakkabe jiragen ta domin tabbatar wa Amurka da karfinta na soji
- Gargadin Koriya ta Arewa na zuwa ne daidai lokacin da wasu jiragen ruwa na kasar Japan biyu ke wani atisaye da jiragen yakin Amurka a yankin yammacin Pacific
Shugaba Donald Trump ya bayar da umarnin wasu manyan jiragen kasar su keta gabar ruwan yankin na Koriya, a martaninta kan yunkurin Koriya ta Arewa na gwada makaman nukiliya da masu linzami.
Legit.ng ta samu labarin cewa ba a dai bayyana takamaiman wuraren da Amurkar ke hari ba a yankin, sai dai kalaman mataimakin shugaban Amurka na Asabar na cewa nan ba da jimawa ba ne jiragen za su isa.
KU KARANTA: Masarautar Kano ta shiga matsala
Koriya ta Arewa ta kuma kama wani dan kasar Amurka da ke kokarin ficewa daga kasar a jiya Lahadi, bayan kasancewar wasu Amirkawa biyu da ke tsare tun farko.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng