Kalli ‘ya’yan marigayi Yar’adua wadda dukkaninsu matan tsofaffin gwamnoni ne
Kyawawan hotunan ‘ya’yan marigayi Yar’adua wanda dukkaninsu mataye ne ga tsofaffin gwamnoni a Najeriya.
Umaru Musa Yar’Adua ya kasance shugaban kasar Najeriya kafin rasuwar sa a shekarar 2010. Ya yi aiki a matsayin gwamnan jihar Katsina kafin ya hau kujerar shugabancin kasa. Yana auren Turai Umaru Yar’Adua sannan kuma sun haifi yara bakwai tare.
KU KARANTA KUMA: Anya wannan ne Buharin da aka sani kuwa- Inji wani Dan Majalisa
Uku daga cikin ‘ya’yan sa mata guda biyar na auren tsofaffin gwamnoni a yanzu. Hotunan matayen tsofaffin shugabannin ya yadu a yanar gizo sannan kuma Legit.ng ta gabatar maku da kyawawan matan.
Dukkaninsu sun fito cikin shiga iri daya yayinda suka dauki hoto tare.
Maryam na auren tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shehu Shema. Nafisat na auren tsohon gwamnan jihar Bauchi, Isa Yuguda yayinda Zainab ta kasance matar tsohon gwamnan jihar Kebbi, Usman Saidu Nasamu Dakingari.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Legit.ng ta hadu da wani matashi wanda ya iya zane sosai
Asali: Legit.ng