Dalibar makaranta ta rasa idonta bayan harin da malami ya kai mata, amma kwararru sunce naira miliyan 1 zai iya dawo da ganinta

Dalibar makaranta ta rasa idonta bayan harin da malami ya kai mata, amma kwararru sunce naira miliyan 1 zai iya dawo da ganinta

Mahaifin wata dalibar makarantar karamar sakandare mai shekaru 14 wacce malami ya lalata ma ido sanadiyar zuba mata bulala a ido ya koka kan neman abi masa hakkin sa da kuma taimako don nema mata magani.

Idon Raliya Suleiman na dama ya samu matsala ne lokacin da malaminta ya doketa ta hanyar yin amfani da wani bulala da aka nannade da karfe.

Dalibar makaranta ta rasa idonta bayan harin da malami ya kai mata, amma kwararru sunce naira miliyan 1 zai iya dawo da ganinta
Ralia Suleiman

Mahaifinta, Suleiman Umar Kachia, wani manomi a Kachia, karamar hukumar Kachia dake jihar Kaduna, ya yi bayanin al’amarin a ranar Litinin a asibitin gyaran ido na kasa, dake Kaduna inda take samun kulawa.

A ranar 23 ga watan Fabrairu mallam Suleiman yace malamin, Moses Auta, wanda ya kasance malamin ladabtar da dalibai yayi amfani da zabori dake nannade da karafuna gurin dukar ‘yar ta sa.

KU KARANTA KUMA: Gargadi: hukumar soji zata gwada abubuwan fashewa, sun gargadi mazauna yankin

“Na kai rahoton al’amarin ga hukumar yan sandan Kachia. Shi (malamin) ya kaita babban asibitin Kachia, inda aka tura mu zuwa asibitin ido na kasa dake Kaduna.

“Asibitin idon sunce ruwan idonta ya rigada ya tsiyaye don haka bazata iya gani da idon ba. Maganin da zasu iya yi mata kawai shine su daidaita kwayar idon daga fadawa cikin kokon kanta da kuma dakatar da tsiyayan da yake yi.” Cewar sa.

A halin da ake ciki, mallam Suleiman ya ce kwararru a wani asibiti mai zaman kansa dake Kaduna, Thelish Eye Clinic, sunce zasu iya dawo mata da ganinta, “amma sun bukaci a dire masu naira miliyan daya.

“A ina zan zamu miliyan daya? Koda na siyar da gidana da dukkan amfanin gonana, ba zai kai yawan wannan kudin ba. Yan uwana ne ma suke biyan kudin maganinta a yanzu.

“Ina rokon gwamnatin jihar Kaduna, yan sanda da sauran hukumomi da masu fada a ji a Najeriya da su taimaka su kawo mana dauki.

“Muna kuma rokon hukuma da ta kwatan mana yanci daga malamin da ya fasa ma yata idonta guda daya sannan kuma yake yawo a gari kamar babu abunda ya faru,” ya kara da cewa.

Da take bayanin yadda al’amarin ya faru, Ralia wacce idonta ke lullube da auduga ta bayyana cewa malamin, wanda ke karantar da su darasin kimiyya, ya kirasu su 20 a wannan rana wanda suka hada da shugaban dalibai, da su same shi a dakin karatu.

“Ya umarce mu gaba daya da mu yi birgima a kasa, sannan ya fara dukan mu da bulala da aka daure da karafuna.

KU KARANTA KUMA: Rikicin PDP: Gwamna Dickson da IBB na cikin ganawar sirri

“Na fada mai cewa bani da lafiya kuma ina da raunuka a baya na, amma ya nace sai ya doke ni har sai da ya buga mun a idona na dama sannan jinni ya fara zuba daga ciki. Sauran dalibai suka fara ihu, amma yaki daina wa har sai da wata malama tayi gaggawan dakatar da shi.

“Likitoci sunce bazan kara gani da wannan idon ba kuma, har sai an kaini kasar waje don samun kula na musamman."

Kakakin yan sandan jihar Kaduna, Aliyu Usman, ya tabbatar da faruwar al’amarin.

“An kawo rahoton al’amarin ga hukumar yan sandan Kachia kuma a yanzu ana nan ana gudanar da bincike,” cewar Mista Usman.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng