An yi sulhu da yan bindiga a jihar Zamfara

An yi sulhu da yan bindiga a jihar Zamfara

-Mutanen da 'yan bindigan suka sace su fiye da araba'in akan hanyarsu ta zuwa kasuwa ranar Juma'ar da ta gabata a yankin Dansadau cikin karamar hukumar Maru sun samu 'yancinsu ne biyo bayan wani sulhu da aka yi

-An samu yin sulhu da 'yan bindigan ne tsakanin kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa a karkashin shugabancin mataimakin gwamnan jihar da kuma 'yanbindigan

An yi sulhu da yan bindiga a jihar Zamfara

[caption id="attachment_890384" align="alignnone" width="300"] President Muhammadu Buhari in Gusau, Zamfara state[/caption]

To saidai gwamnatin jihar kawo yanzu bata fito fili tayi wani cikakken bayani ba akan sulhun amma rahotanni sun nuna cewar 'yan bindigan sun bukaci a mayar masu da shanunsu da aka kwace kafin su sako mutanen. Bisa ga alamu gwamnati ta cika wannan sharadin na 'yan bindigan.

Ku Karanta: An sake kubuto wasu da yan Boko Haram suka sace

Yayinda yake gabatar da mutanen ga gwamnan jihar Zamfara mataimakin gwamnan yace ya koyi babban daratsi a jagorancin kwamitin 'yanto mutanen da yayi.

Mataimakin gwamnan ya kira shugabannin sassa, da shugabannin siyasa, da jami'an tsaro cewar idan ana son zaman lafiya da kwanciyar hankali to su nisanci zalunci. Yace abu na biyu da ya koya shi ne ta hanyar tattaunawa ana iya samun zaman lafiya tare da warware duk wata matsala.

Duk da cewa sai da nuna karfi ake shawo kan mazalunta cewa akwai hukuma amma karfi kawai baya kawo zaman lafiya sai an hadashi da lumana da jawo hankali.

Wannan sulhun da gwamnati tayi ya kara jaddada zargin da wasu keyi na cewa gwamnati nada masaniya akan inda 'yanbindigan suke. Wani yace gwamnati ta je wajen sojoji ta karbi shanun ta kaiwa 'yanbindigan kana ta amshi mutanen. Wai sun nuna kamar babu gwamnati. Yace babu wanda ya raka mataimakin gwamnan kuma tun karfe goma na safe da aka shirya bai je ba sai karfe takwas na dare.

A nashi bangaren gwamnan jihar yana zargin wasu da hannu cikin ruruta wutar rikici a jihar. Ya kira jami'an tsaro su tsaya suyi aikinsu yadda ya kamata. Injishi sarakuna su dinga sa ido kana alamuran tsaro saboda aiki ne na hadin gwuiwa.

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng