Dan shekara 13 yayiwa malamarsa ciki

Dan shekara 13 yayiwa malamarsa ciki

Alexandar Vera, wata tsohuwar malamar makaranta wacce ke yawan jima’I da dalibinta mai shekaru 13 ta amsa laifinta

Ta amsa laifinta a ranar Laraba kan lalata wani yaro inda ta mayar da shi abun hutun ta.

Vera ta hadu da yaron mai shekaru 13 wanda ya kasance dalibinta da take koyarwa darasin turanci a lokacin makarantar rani, a cewar takardun kotu.

Tashar labaran ABC ta ruwaito cewa alaka na jima’I ya kullu a tsakaninsu tun daga lokacin.

Dan shekara 13 yayiwa malamarsa ciki
Alexandar Vera a Kotu

Vera tayi ikirarin cewa ita da matashin na soyayya ne, kuma ya gabatar da ita ga yan uwansa a matsayin budurwar sa, takardan kotu ta bayyana. An rahoto cewa iyayen yaron sun amince da soyayyar, har ma da yan uwan Vera da suka taru.

KU KARANTA KUMA: Shaida ya tona asirin Fayose a shari’ar rashawa da ake ciki

Takardun kotu sun bada cikakken bayani kan yadda Vera tayi ciki da dan karamin yaron a watan Janairu, an kuma ce yan uwansa sun ji dadi sosai tare da goyon baya ga yaron.

A halin yanzu, hukumar kula da yara sunyi wa makarantar ziyarar bazata a watan Fabrairu suka kuma yi tambaya game da alakarsu. An rahoto cewa wannan ya tsorata ta taje ta cire cikin.

A yanzu yaron na karkashin kulawa.

Ana sa ran Vera ta koma kotu don a yanke mata hukunci a watan Janairu

Asali: Legit.ng

Online view pixel