Sojoji sun dakile wani babban bala'i a garin Maiduguri

Sojoji sun dakile wani babban bala'i a garin Maiduguri

- Rahotanni daga birnin Maiduguri na jihar Borno da ke Najeriya na cewa an kashe wasu 'yan kunar-bakin-wake da suka yi yunkuri tayar da bama-bamai da safiyar Juma'a.

- Jamai'an tsaro sun shaida wa majiyar mu cewa maharan uku, wadanda dukkan su mata ne, sun yi yunkurin shiga birnin Maiduguri ne amma an ci lagonsu aunguwar Ummurari da ke wajen birnin.

Kungiyar Boko Haram ce dai ke kai hare-hare a birnin da ma wasu yankuna na jihar ta Borno da makwabtan jihohi.

Sai dai rundunar sojin Najeriya ta ce tana ci gaba da fatattakar mayakan kungiyar, kuma nan ba da dadewa ba za ta kawar da ita daga doron kasa.

Sojoji sun dakile wani babban bala'i a garin Maiduguri
Sojojin Najeriya

Ko a makon jiya sai da mayakan kungiyar suka kashe wasu sojin Najeriya, cikin su har da Latftanar Kanar Muhammad Abu Ali, wani soja da ya yi suna wajen ragargazar mayakan Boko Haram.

A wani labarin kuma, Dakarun sojojin Nijeriya dake garin Kangarwa a karamar hukumar Kukawa dake jihar Borno sun yi nasarar kashe 'yan Boko Haram guda 13 a yayin wata farauta da suka fita, inda wasu daga cikin 'yan Boko Haram din da dama suka tsira da harbin bindiga.

Saidai soja daya ya rasa ransa a yayin artabun, yayin da guda uku suka samu rauni.

Ku Karanta: Majalisar dattijai ta tozarta hukumar tara haraji ta FIRS

Sojojin sun kuma yi nasarar karbe makamai da motacin 'yan bindigan a yayin artabun wanda aka dauki tsawon awanni hudu ana fafatawa.

A makon da ya gaba ne dai hukumomin sojin Najeriya suka gudanar da jana'izar kwamandan rundunar sojin kasar ta 272 mai kula da tankokin yaki, Laftanar Kanar Muhammad Abu Ali, tare da wasu sojoji hudu.

Kwamandan da sauran sojojin hudu sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suke kokarin dakile wani harin da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai kan barikin sojin kasar na 119 da ke garin Malam Fatori a Jihar Borno.

Haka ma wasu sojojin hudu sun samu raunukka yayin da mayakan Boko Haram 14 suka halaka a cikin artabun na yammacin ranar Asabar.

A shekara ta 2015 ne Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar Janar Tukur Buratai, ya yi wa Muhammad Abu-Ali karin girma daga Manjo zuwa Laftanar Kanar tun kafin ya kai shekarun samun karin girman, saboda jaruntar da ya nuna da ta kai ga kwato yankuna da dama daga hannun mayakan na Boko Haram.

Karshen satin da ya gabata ne dai Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar Laftanar Kanar Muhammad Abu Ali, tare da wasu sojojin hudu, lokacin da suka dakile wani harin mayakan Boko Haram a kan barikin sojin kasar na 119 dake Mallam Fatori, jihar Borno.

Laftanar Kanar Muhammad Abu Ali, shi ne kwamandan runduna ta 272 mai kula da tankokin yaki.

Saboda jarumtarsa ne, a 2015 a Gamboru Ngala, babban hafsan sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai ya yi mushi karin girma daga Manjo zuwa Laftanar Kanar tun kafin ya kai shekarun samun karin girman.

Cikin wata sanarwa, kakakin rundunar sojin kasa ta kasar, Kanar Sani Uman Kukasheka, ya ce sojojin sun kashe mayakan Boko Haram din goma sha hudu a lokacin artabun.

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: