‘Dan wasan Real Madrid ya tsokano fada, yi kaca-kaca da Kungiyoyin FIFA da UEFA

‘Dan wasan Real Madrid ya tsokano fada, yi kaca-kaca da Kungiyoyin FIFA da UEFA

  • Thibaut Courtois ya yi kaca-kaca da FIFA da UEFA bayan gasar Nations league
  • ‘Dan kwallon na Belgium yace kungiyoyin kwallo sun fi damu wa da kudin-shiga
  • Courtois yace ana buga wasanni barkatai ne saboda kudin da UEFA za ta samu

Italy - ‘Dan wasan kwallon kafan da ke tsare ragar kasar Belgium, Thibaut Courtois ya zargi shugabannin kwallo na Duniya da zafin neman kudi ido rufe.

Courtois yace an fi maida hankali a kan kudin da za a samu, a maimakon lafiya da walwalar ‘yan wasa.

Sky Sports ta rahoto Thibaut Courtois yana Allah-wadai da jadawalin wasannin da ake buga wa. Tauraron mai shekara 29 ya koka ne bayan wasansu da Italiya.

A karshen makon da ya gabata ne kasar Italiya ta doke Belgium da ci 2-1 a wasan fitar da wanda ya zo na uku a gasan UEFA Nations league na kasashen Turai.

Kara karanta wannan

Kotu ta bada umarni a daure ‘Dan wasan Bayern a kurkuku saboda tsohon rikici da Budurwarsa

Wasan je-ka-na-yi-ka

Courtois yana ganin cewa wannan wasa bai da wani amfanin kirki. Rahoton yace gajiya ta hana Eden Hazard da Romelu Lukaku buga wasan na su da Italiya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

‘Dan wasan Belgium
Belgium v Italy, UEFA Nations league Hoto: www.managingmadrid.com
Asali: UGC

“Kudi kurum ake nema da wannan wasa, kuma dole mu fadi gaskiya a kai.”
Mun buga wasan ne kurum saboda UEFA za ta samu karin kudi.” - Courtois.

Legit.ng Hausa ta fahimci ‘Dan wasan na Real Madrid ya buga duka wasannin da Belgium ta buga. Tauraron ya koka, yace ‘yan wasan kwallon ba karafuna ba ne.

“Dubi yadda kasashen suka canza ‘yan wasan da suka buga. Idan da ace sun kai wasan karshe ne, da wasu ‘yan kwallon dabam ne za su buga wasan.”
“Hakan ya nuna cewa muna buga wasanni da yawa.” Inji Courtois.

Saudi Arabian Public Investment Fund sun saye Newcastle

Kara karanta wannan

An kashe mutane fiye da 1, 300 yayin da Fadar Shugaban kasa ke cewa ana samun tsaro

Kun samu labari bayan cinikin Newcastle da aka yi tsakanin Mike Ashely da Saudi Arabian Public Investment Fund, teburin dukiyar kungiyoyin kwallo ya canza.

A halin yanzu babu kungiyar da ta kai Newcastle da ke wasa a kasar Ingila arziki. Wadanda suka mallaki kungiyar ta Newcastle sun ba fam Dala biliyan 400 baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel